Kainuwa logo Kainuwa logo

Sirrin Crypto By Nasir I Mahuta

Free

In Stock

ABOUT THIS BOOK
kasuwancin cryptocurrency na ci gaba da haɓaka gami da mamaya tamkar wutar jeji, mutane a sassa daban-daban na faɗin duniya na tururuwar shiga kasuwancin. Adadin masu amfani da cryptocurrency kullum ƙaruwa ya ke duk da matsin lamba da ƙoƙarin yaƙi da shi da Gwamnatocin wasu ƙasashen ke yi. Alherin da a ke samu a kasuwancin ya sa al'umma ke tururuwar shiga domin ka da a yi babu su, wanda suka jima a cikin kasuwancin za ka iya ganin alherin a bayyane tare da su. 
Babban abin ƙayatarwa da kasuwancin crypto shi ne, saye da sayarwar duka yana faruwa ne akan internet. Ta hanyar amfani da wayar da ke hannunka kana iya zama babban Ɗan kasuwa, kana zaune a cikin ɗakinka ba tare da ka je ko ina ba za ka iya samun maƙudan kuɗaɗe. 
Idan kai ma'aikaci ne,kasuwancin crypto ba zai hana ka yin aikin ka ba domin za ka iya gudanar da kasuwancin kana a wajen aikinka ko bayan ka koma gida. Hatta Ƴan kasuwar da ke kasuwancin zahiri, ɗalibai da ke karatu, malamai da ke koyarwa a makarantu, matan gida, tsoffi da 
gajiyayyu duka za su iya gudanar da kasuwancin a duk inda su ke. Ashe kuwa, kasuwancin crypto zai taimaka sosai wajen rage yawan marasa aikin yi musamman a nan arewacin Nijeriya. 
 

Customer Reviews

Please log in to leave a review.

No reviews for this product yet.

Dismiss